<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>340</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Ubangiji, Allahnmu, ka sa albarkarka
 Yanzu a bisa shugabanni da dukan iyalansu.

[V2]
 2) Ka ƙara musu aminci, alheri da soyayya.
 Salama duk da lafiya su daɗu a mulkinsu.

[V3]
 3) Ka ba su ruhun hikima da ruhun ganewa.
 Ka kafa dukan maganarsu bisa ga shari'arka.

[V4]
 4) Domin a cikin mulkinsu, kome da za su yi
 Shi daidaita da nufinka, nufi mai tsarki.

[V5]
 5) Hakanan mu jama'arsu, mu riƙa yin godiya
 Gare ka kullum, har da su, a cikin duniya duk.

[V6]
 6) Ya Allah Uba, Allah Ɗa, Allah Ruhu kuma,
 Mu ba ka dukan daraja, ya Allah Triniti.</lyrics>
<title>Ya Ubangiji, Allahnmu, Ka Sa Albarkarka LW340</title>
</song>